Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya ce babu wata kabila da za ta zama koma baya
2020-06-09 11:06:26        cri
Sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, Xi Jinping, ya yi rangadi a jihar Ningxia a jiya Litinin, inda ya tattauna da mazauna yankin Jinhua yuan na gundumar Litong dake birnin Wuzhong. Shugaba Xi ya ce dukkan kabilu al'ummar kasar Sin ne, kuma ba yadda za a yi kasa ta rayu ba tare da yaki da talauci da samar da al'umma mai wadata ta kowacce fuska da kuma wayewa ba. Ya ce dukkan al'umma na aiki ne kafada-da-kafada, wanda yake nuna shekaru dubu 5 na wayewar kan Sinawa da karfin tsarin gurguzu mai halayyar musammam ta kasar Sin.

Jihar Ningxia ta kabilar Hui, daya ne daga cikin jihohin kasar Sin 5 masu cin gashin kansu, inda kuma ke da kabilu da dama kamar Han da Hui da Uygur. Yankin Jinhua yuan na birnin Wuzhong da shugaba Xi ya ziyarta, na da mazauna na dindindin 13850, wadanda kusan rabinsu 'yan kananan kabilu ne. Bisa jerin manufofin shugabanci da kirkire-kirekire, yankin ya zama wani abun misali na hadin kai da ci gaban kabilun kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China