Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya yi kira ga gudunmuwar Sin da Faransa wajen yaki da COVID-19 a duniya
2020-06-06 15:43:35        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga gudunmuwar hadin gwiwar Sin da Faransa wajen cin nasarar yakin da duniya ke yi da annobar COVID-19.

Da yake tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, shugaba Xi Jinping ya ce, akwai bukatar kasashen Sin da Faransa, su ci gaba da taimakawa kasashen duniya a yaki da annobar, inda ya ce tun bayan barkewar cutar, kasashen biyu ke hada hannu wajen yaki da ita.

Da yake bayyana yadda aka gaza dakile bazuwar cutar kamar yadda ya kamata a duniya, ya ce hadin gwiwa da goyon bayan juna, su ne hanyoyi mafi dacewa.

Xi Jinping ya kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su inganta hada hannu wajen bincike da mara baya ga duniya a kokarin samar da riga kafi da magani, da inganta aiwatar da matsayar da aka cimma yayin babban taron kiwon lafiyar duniya karo na 73, da kuma kara mara baya ga hukumar lafiya ta duniya WHO.

Har ila yau, Xi Jinping ya ce, ya kamata kasashen biyu su kara hadin gwiwa tsakaninsu da nahiyar Afrika dangane da yaki da COVID-19. Yana mai cewa, ya kamata Sin da Faransa su martaba tsarin huldar kasa da kasa da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China