Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi:Kafa tsarin kiwon lafiyar jama'a domin kare tsaron rayukan al'ummu
2020-06-02 21:26:26        cri

A yammacin yau Talata babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiyar kasar Xi Jinping, ya jagoranci taron tattaunawa na kwararru, inda ya jaddada cewa, tsaron al'ummun kasa abu ne mafi muhimmanci ga tsaron kasa, don haka dole ne a kafa tsarin kiyaye kiwon lafiyar jama'a, kuma a kyautata tsarin yin gargadi kan aukuwar abubuwa na ba zata, haka kuma a daga matsayin kandagarkin cuta, ta yadda za a tabbatar da tsaron lafiyar al'ummun kasar.

Yayin taron, masani a fannin cutar numfashi na jami'ar koyar da ilmin likitanci ta birnin Guangzhou dake lardin Guangdong Zhong Nanshan, ya da sauran kwararrun likitoci sun gabatar da jawabai, daga baya babban sakatare Xi Jinping, shi ma ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, bayan aukuwar annobar COVID-19, kwamitin tsakiya na JKS ya dauki matakan da suka dace domin ganin bayan cutar a kan lokaci, haka kuma yana mayar da tsaron rayukan al'ummun kasar a gaban komai, har ta kai a yanzu haka an samu sakamako mai gamsarwa.

Xi ya yi nuni da cewa, tsarin riga kafin cututtuka zai samar da tabbaci ga tsaron rayukan jama'a, da tsaron kiwon lafiyar jama'a, da kuma ci gaban zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasa, don haka ya dace a kara mai da hankali kan wannan aiki, tare kuma da zuba karin jari a cikin sa, ta yadda za a kyautata ayyukan samar da hidima a bangaren kiyaye kiwon lafiyar jama'a, tare kuma da kyautata tsarin sa ido kan cututtuka masu yaduwa, da al'amuran kiwon lafiyar jama'a da za su auku ba zato ba tsamani.

Xi ya jaddada cewa, tun bayan barkewar annobar, har kullum kasar Sin tana nacewa kan manufar gina kyakkyawar makomar bil Adama. A sa'i daya kuma tana sauke nauyin kasa da kasa dake bisa wuyanta, haka kuma tana gudanar da hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya, da sauran kasashen da abun ya shafa, ta hanyar samar da bayanan dake shafar kwayar cutar, da dabarun dakile annobar, kana tana samar da tallafin kayayyaki da fasahohi ga kasashen duniya sama da 100 gwargwadon karfinta. Nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar gani wajen samar da kayayyakin kiwon lafiya ga kasashen da suke bukata, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar kiwon lafiyar bin Adama a fadin duniya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China