Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sashen dakon kayayyaki ta jirgin kasa na jihar Xinjiang ya samu karin hada hada
2020-04-06 16:50:57        cri
Hukumar dake lura da zirga-zirgar jiragen kasa ta jihar Xinjiang mai cin gashin kansa, dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta ce hada hadar dakon hajoji da aka yi ta jiragen kasar yankin a watanni ukun farkon shekarar bana, ta kai ta sama da tan miliyan 40.3, adadin da ya karu da kaso 16.1 bisa dari a shekara guda.

Sashen sufurin jiragen kasa na Xinjiang ya koma bakin aiki gadan gadan, tun bayan da kasar Sin ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Kawo yanzu sassan layukan dogo na Xinjiang na ci gaba da fadada harkokin cinikayyar su yadda ya kamata.

Rahotanni daga hukumar dake lura da sufurin jiragen kasa ta jihar sun nuna cewa, a watan Maris da ya gabata, adadin jiragen kasa na dakon kaya a jihar, wadanda suka koma bakin aiki sun kai 37, sun kuma yi dakon kayayyakin bukatun yau da kullum, da ma sauran nau'o'in hajoji da dama a yankin, wadanda yawansu ya kai tan 39,600.

Kamfanin sufurin jiragen kasan yankin, ya ce yana gudanar da tsarin sufuri mai dacewa da dakon nau'o'in hajoji iri daban daban, da kayan sarrafawa a masana'antu, ta yadda hakan zai samar da zarafin inganta harkar sufurinsa yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China