Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaran dake yankunan karkarar Xinjiang suna cin gajiyar tsarin makarantun reno
2020-06-02 10:11:25        cri
Rahotanni daga yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, sun bayyana cewa, yaran dake zaune a yankunan karkarar jihar, na kara cin gajiyar tsarin nan na makarantar reno, biyo bayan makuden kudaden da mahukuntan yankin ke kara zubawa a bangaren ilimi.

Wata sanarwar da aka fitar bayan kammala wani taron manema labarai a jiya Litinin, ta bayyana cewa, yankin na Xinjiang, ya zuba kudade masu tarin yawa a fannin gine-gine da gyara da fadada makarantun reno kimanin 4,408 a yankunan karkarar yankin.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka dukkan yara masu shekaru 4 zuwa 6 da suka isa shiga makarantun reno a yankin mai cin gashin kansa, suna samun ilimi a irin wadannan makarantun reno, baya ga abincin rana da 'ya'yan itatuwa da kayan ciye-ciye da ake ba su kyauta.

Hukumomin yankin sun bayyana cewa, a shekarar 2019, yankin na Xinjiang ya kashe Yuan biliyan 86.31 a fannin ilimi, karuwar kimanin Yuan biliyan 4.77 ko kaso 5.85 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China