Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin tsare musulmai cikin kurkukun Sin ba shi da tushe
2020-04-03 20:42:08        cri
A yau a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, ya dace wasu 'yan siyasar Amurka su daina hada annobar cutar numfashi ta COVID-19 da batun siyasa, su kuma daina shafawa kasar Sin kashin kaji.

A jiya jakadan hukumar kula da 'yancin addinin kasa da kasa ta ma'aikatar harkokin wajen Amurka Sam Brownback ya bayyana cewa, an tsare wasu mutane da dama a cikin kurkuku bisa dalilin addini, ciki har da musulmai sama da miliyan daya a yankin Xinjiang, inda ya yi kira ga gwamnatin kasar Sin da ta sake su a lokacin da ake kokarin dakile annobar COVID-19, kan batun, madam Hua ta karyata zargin a gun taron ganawa da manema labarai cewa, "Zargin ba shi da tushe ko kadan, kasar Sin ta samu sakamako bayan kokarin da take yi na yaki da annobar, lamarin da ya kare lafiyar al'ummar kasar, ciki har da musulmai, haka kuma matakin ya taka rawa wajen kiyaye tsaron lafiyar jama'a a fadin duniya, kuma duk wadannan sun riga sun samu amincewa daga daukacin al'ummomin kasa da kasa, amma wasu 'yan siyasa na Amurka kamar Brownback sun ki amincewa da haka."

Madam Hua ta yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin tana martaba 'yancin bin addini na 'yan kasarta bisa doka, al'ummmar kasar 'yan kabilu daban daban suna jin dadin 'yancin bin addini, a kasar Sin, babu wadanda aka tsare bisa laifin addini, balle ma a tsare musulmai sama da miliyan daya a cikin kurkuku a yankin Xinjiang.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China