Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sassauta ka'idojin ciniki a tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan na kasar Sin
2020-06-08 16:36:52        cri
A yau da safe, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labaru, inda aka yi bayani game da shirin gina tashar yin cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan.

Game da hakan shugaban lardin Hainan Shen Xiaoming, ya bayyana cewa, za a yi kokarin samar da sauki, da 'yanci, a fannin zuba jari a tashar yin cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan, da aiwatar da manufar soke yin bincike, da amincewa da gwamnatin lardin ke yi, muddin babu wasu ka'idoji ko dokokin da ya wajaba a yi aiki da su.

Kamfanoni za su iya yin rajista da yin alkawari kai tsaye, da fara gudanar da ayyukansu idan sharadi ke cika. Hakazalika kuma, za a gudanar da manufofin nuna matsayin daidaito ga jarin waje kafin masu su, su soma zuba jari, da kuma daidaita takardar sassan da baki ba za su iya zuba jari a ciki ba a tashar.

Kaza lika kamfanonin dake ayyuka masu nasaba da kaimi ga gina tashar, irin wadannan kamfanoni za a soke musu haraji daga ribar da aka samu karkashin jarin waje da suke zubawa kai tsaye. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China