Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Kaddamar Da Bikin Sayayya A Birnin Beijing
2020-06-07 16:44:45        cri

A jiya Asabar, babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da gwamnatin birnin Beijing, sun yi hadin gwiwa wajen kaddamar da wani gagarumin bikin sayayya, da zummar taimakawa farfado da kasuwanci da ayyukan hidima, bayan da aka samu shawo kan yaduwar cutar COVID-19.

A nata bangaren, gwamnatin birnin Beijing ta raba takardun tallafawa masu sayayya da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan biliyan 12.2, da gabatar da wasu manufofi na sa kaimi ga sayen kayayyaki.

A wajen bikin kaddamar da shirin na habaka aikin sayayya, rukunin CMG ya sanya wasu shahararrun masu jagorantar shirye-shirye taimakawa tallace-tallacen kayayyaki, ta kafar shafukan Intanet da telabijin, inda yawan darajar kayayyakin da aka sayar cikin wasu sa'o'i 3 ya kai kimanin Yuan biliyan 1.4.

Za a ci gaba da gudanar da bikin sayayyar har zuwa karshen wannan shekara, don cimma muradun kasar na habaka aikin ciniki da kasuwanci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China