Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana ba da gudunmawa sosai wajen kiyaye muhallin duniya
2020-06-05 14:14:47        cri

Yau Juma'a rana ce ta kiyaye muhalli ta kasa da kasa, jigon ranar ta wannan shekara shi ne "Tabbatar da kasancewar halittu daban daban a duniya".

Jami'an hukumar kare muhalli ta MDD wato UNEP sun bayyana sau da dama cewa, Sin tana hada kanta da kasashen Afrika wajen kiyaye tsirrai da dabbobin daji. A shekarun baya-bayan nan kuma, ta kafa doka dangane da laifuffukan gurbata muhalli da hana haramtaccen ciniki a wannan fanni, abin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ba za ta yarda da kowane laifi da za a aikata dangane da gurbata muhalli ba.

Baya ga matakan da gwamnatin ke dauka, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikon mutane, su ma suna shiga wannan aiki. Wasu kamfanoni masu jarin Sin sun kafa asusun kiyaye muhalli don tallafawa ma'aikatan kiyaye namun daji a nahiyar Afrika, matakin da ya samu yabo sosai daga kasashen na Afrika.

Ban da kiyaye dabobbi, Sin tana kuma amfani da dabarunta na kiyaye muhalli. Alal misali shirin "Babbar ganuwa mai launin kore" dake karkashin jagorancin AU, yana maida hankali wajen kawar da mummunan tasiri da kwararowar hamada ke kawowa al'umma da tattalin arziki da kuma muhalli a yankin Sahel da Sahara.

Haka zalika, fasahar Juncao da Sin take mallaka ita ma ta yadu zuwa jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, da Fiji da kuma Laos da Lesotho da dai sauran kasashe da yankuna fiye da 100. A matsayin babban sakamakon da aka samu a taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na shekerar 2018, wannan fasaha dai ta yadu zuwa jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya a watan Maris na shekarar 2019, kuma an horas da 'yan Afrika ta Tsakiya sau biyu a Fuzhou da Bangui karkashin taimakon gwamnatin kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China