Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Aikin tantance bola a wasu manyan birane 46 ya kai fiye da kashi 70%
2020-06-05 13:44:11        cri

Yau rana ce ta kiyaye muhalli ta kasa da kasa, jigon ranar a kasar Sin na wannan karo shi ne "Zan dauki mataki don ganin kasar Sin ta zama mai kyan gani", a daidai wannan lokaci, ya kamata a mai da hankali kan aikin tantance bola.

Tun a watan Maris na shekarar 2017, ma'aikatar gidaje da raya birane da kauyuka ta kasar Sin ta mayar da wasu manyan birane 46 a matsayin wuraren gwaje-gwajen aikin tantance bola. Ya zuwa yanzu, an gudanar da wannan aiki yadda ya kamata a wuraren, kuma aikin da aka gudanar a wuraren ya kai fiye da kashi 70%. Ban da wannan kuma, yawan sharar gine-gine da ta lambun shan iska ya ragu sosai a Guangzhou da Suzhou da kuma Xi'an da sauran wurare. Kana yawan bolar da aka tara aka yi jigilarsu ya ragu matuka a Shanghai da Xiamen da sauransu. Haka kuma, yawan bolar da ake iya sake yin amfani da su kamar gilas da takardu da dai sauransu da aka tantance ya karu sosai.

Wani jami'i a ma'aikatar ya nuna cewa, an kiyasta cewa, ya zuwa karshen wannan shekara, yawan bolar abincin da wadannan birane 46 za su iya tantancewa zai kai ton 65000 a ko wace rana, adadin da ya dace da bolar da ake fitarwa a rana. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China