Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afirka ya zarta dubu 130
2020-05-31 15:44:09        cri

A jiya Asabar 30 ga wata, alkaluman da cibiyar CDC ta Afirka ta fitar sun nuna cewa, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya kai 136,677, a cikinsu, mutanen da suka rasa rayuka sakamakon cutar sun kai 3941, kana wadanda suka warke sun kai 56,958.

A wannan rana kuma ma'aikatar kiwon lafiya da aikin zamantakewar al'umma ta kasar Senegal ta bayyana cewa, hukumomin gwamnati daban daban na kasar ta Senegal za ta dauki karin matakan dakile annobar a yankunan Dakar, saboda yawancin masu kamuwa da cutar wato kashi 3 bisa 4 suna rayuwa a wuraren ne.

Haka zalika, mataimakin shugaban cibiyar nazarin kiwon lafiya ta kasar Mozambik ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya a jiya cewa, a halin yanzu ana gudanar da bincike kan yanayin barkewar annobar da kasar ke ciki, domin hana yaduwarta a kasar a kan lokaci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China