Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin da cutar COVID-19 ta fi kamari a Afrika ta kudu zai dauki sabbin jami'an lafiya
2020-06-07 16:17:56        cri
Lardin yammacin Cape na kasar Afrika ta kudu, inda annobar COVID-19 ta fi kamari, a ranar Asabar ya sanar da bukatar neman daukar sabbin ma'aikatan jiyya kimanin 5,272 yayin da yawan masu kamuwa da cutar ke kara hauhawa a yankin.

A wata sanarwar da jagoran yankin na yammacin Cape Allan Winde, ya fitar ya ce, tilas ne a yi kokarin shawo kan matsalar karancin jami'ian lafiya a lardin kafin annobar ta kai matsayin koli.

Winde ya ce, lardin yana ci gaba da yin aiki tukuru domin samar da karin sabbin gadaje a asibitoci domin zama ciki shiri tun gabanin annobar ta kai matsayin koli.

A ziyarar da ya kai yankin ranar Juma'a, shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya yi alkawarin shawo kan matsalar karancin ma'aikatan jiyyar.

A cewar Ramaphosa, kudi ba wata matsala ba ce, ya kara da cewa, za'a samar da dukkan bukatun da yankin yammacin Cape yake nema domin tinkarar yanayin karin yaduwar annobar da ake fuskanta.

Ramaphosa ya bada izini ga gwamnatin Western Cape ta dauki karin likitoci da ma'aikatan jiyya domin taimakawa wajen shawo kan matsalar karuwa masu kamuwa da cutar COVID-19 a asibitocin yankin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China