Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin ruwan Afirka ta kudu tana yin atisaye tare da takwarorin ta na Rasha da Sin
2019-11-26 10:59:58        cri

Dakarun rundunar sojojin ruwan Afirka ta kudu, suna yin atisaye a teku tare da takwarorin su na kasahen Rasha da Sin, a yankin tekun kudancin kasar dake daura da birnin Cape Town. Wannan ne karon farko da wadannan kasashe uku suka yi atisayen sojin ruwa a tarihi.

Yayin atisayen da ya gudana tsakanin ranekun 25 zuwa 30 ga watan Nuwambar nan, sojojin za su maida hankali ga ayyukan samar da tsaro ga sashen tattalin arzikin teku, da aikin hadin gwiwa, da tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin dakarun da suka halarci atisayen.

Ana fatan atisayen na mako guda, zai nuna aniyar da sassan ke da ita, game da tabbatar da tsaron teku, da wanzar da zaman lafiya da daidaito cikin hadin gwiwa.

Rundunar sojojin ruwan Afirka ta kudu, ta ce cikin kwanaki 3 na farko, za a gudanar da atisaye game da tsara ayyuka a teku, da sauran ayyukan soji masu nasaba da zamantakewa da raya al'adu. Sai kuma ayyukan sarrafa bindigogi a teku, da gwajin saukar jirage masu saukar ungulu kan jiragen ruwa, da kuma ayyukan dakon kayayyaki, da atisayen dakile annoba a duk lokacin da aka fuskanci hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China