![]() |
|
2020-06-05 12:57:17 cri |
A cewar SANA, dakarun sojojin saman Syria, sun yi nasarar dakile wasu jerin hare haren makamai masu linzami da aka shirya kaiwa birnin Masyaf dake tsakiyar lardin Hama.
Haka zalika, tashar talabijin ta yankin labarawa, al-Mayadeen TV, ta bada rahoton cewa, wasu jiragen saman yakin Isra'ila sun harba makamai masu linzami daga cikin sararin saman kasar Lebanon.
Rahotannin sun ce, Isra'ila ta shirya kai hare haren mukami mai linzami zuwa wasu yankuna hudu na Syria daga bisani a juya akalarsu zuwa Isra'ilan.
A cewar hukumar dake sanya ido kan hakkin dan Adam a Syria, jiragen saman yakin Isra'ila sun shirya kai hare haren ne kan kamfanonin kera makaman dakarun sojojin kasar Syria dake birnin Masyaf a yammacin lardin Hama na kasar.
Hukumar kare hakkin dan Adam dake da sansaninta a Birtaniya ta ambato cewa, sojojin saman Syria sun yi nasarar dakile hare haren makamai masu linzami masu tarin yawa.
Wannan shine hari na baya bayan nan cikin jerin hare haren da Isra'ila ta sha kaddamarwa a yankunan sojoji na kasar Syria. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China