Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnonin jihohin Amurka sun yi watsi da shawarar Trump na tura sojoji don tarwatsa zanga-zanga
2020-06-03 10:35:40        cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, idan har jihohin kasar suka gaza kwantar da tarzoma dake faruwa a jihohin nasu, to gwamnatin tarayya za ta duba yiwuwar tura sojoji zuwa jihohin domin tarwatsa masu zanga-zangar. Wannan furuci ya fusata gwamnonin jihohi daban-daban, gwamnan jihar Illinois J. B. Pritzker ya nuna cewa, kalaman na Donald Trump ka iya tsananta halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ba ta da ikon tura sojoji zuwa jihohin kasar ba tare da amincewarsu ba.

Shi ma gwamnan jihar Wanshington Jay Inslee ya ba da sanarwa, inda ya zargi Trump cewa, abin da ya fada ya bayyana gazawarsa, a rudanin da aka yi samu a lokacin mulkinsa bai dauki matakin da ya dace ba ban da yada jita-jita da karairayi. Ran 2 ga wata agogon wurin, gwamnan Texas Greg Abbott ya jaddada a wani taron manema labarai cewa, jihar ba ta bukatar gwamnatin tarraya ta tura mata sojoji domin ta shiga tsakani.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China