Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin: Ya dace masu hankali su karyata labaran karya kan Xinjiang
2020-04-01 21:15:30        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta yi kira ga daidaikun jama'a masu hankali, da su nuna adawa da ma karyata labaran karya da ake yadawa game da manufar kasar Sin kan yankin Xinjiang.

Madan Hua ta bayyana haka ne, yayin da ake tambaye ta a taron manema labarai kan rahoton da Grayzone wani shafin intanet na kasar Amurka mai zaman kansa ya wallafa, inda ya ba da shawarar cewa, zargin baya-bayan nan da ake yiwa kasar Sin, game da shirin kasar na "tilastawa fursononi aikin dole", a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa. wata kungiyar Australia dake samun goyon bayan Amurka ne ta fara bullo da shi.

Jami'ar ta ce, wannan na nuna cewa, wasu mutane na gudanar da harkokinsu bisa boyayyar manufa. Mutane da suka san abin da suke yi, da nuna adalci, ya kamata su iya bambance tsakanin karya da gaskiya, su kuma yi aiki tare don yaki da labarin karya kamar wannan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China