Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labaru guda 9 dangane da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kananan yara
2020-06-01 16:02:24        cri

Labari na tara: Lura da yadda ake komawa makaranta

Bayan barkewar annobar COVID-19, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya lura sosai da yadda dalibai ke komawa makaranta don fara harkokin karatu. A ranar 21 ga watan Afrilun bana, yayin rangadin da ya kai a lardin Shaanxi, ya yi tattaki zuwa wata makarantar firamare, don ganewa idanunsa yadda dalibai ke karatu da zama, inda ya karfafa musu gwiwar kara motsa jiki. Shugaba Xi ya kuma gayawa shugabannin makarantar da su mayar da hankali wajen kara fesa maganin kashe kwayoyin cuta, da samar da tsaro ga daliban.

Albarkacin ranar yara ta duniya ta bana, wato a ranar 31 ga watan Mayu, shugaba Xi ya taya daukacin yaran kasar Sin murnar wannan rana, inda ya ba su shawarar mayar da hankali kan harkokinsu na karatu, da kara motsa jiki.

Har kullum shugaba Xi ya bayyana cewa, babban burinsa shi ne ganin yadda yaran kasar suke samun ci gaba yadda ya kamata.


1  2  3  4  5  6  7  8  9  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China