Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labaru guda 9 dangane da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kananan yara
2020-06-01 16:02:24        cri

Labari na shida: Wasikun da yaran Australia suka aika wa shugaba Xi da uwargidansa

A shekarar 2014, daliban makarantar firamare guda 16 dake jihar Tasmania ta kasar Australia,

sun aika wata wasika ga shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan,

inda suka bayyana kyakkyawan yanayi da muhallin halittu na wurin,

sun kuma gayyaci shugaba Xi da uwargida Peng da su kai ziyara wurin da Sinanci.

Amma ba su taba zaton cewa,

Da gaske, wasikarsu ta kawo shugaba Xi da uwargida Peng gabansu.

A matsayinsu na baki na musamman,

wadannan kananan yara sun halarci bikin maraba da aka shiryawa shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan.

A gaban wadannan kananan yara,

Xi Jinping ya yi murmushi ya gaishe su,

ya kuma yi fatan cewa, za su koyi Sinanci sosai da kuma kara sanin al'adu da tarihin Sin.

Haka kuma, sun shuka wani itace na zumunci.

Xi Jinping ya ce,

"Za mu shuka iri na zumunci a tsakanin Sin da Australia,

Har ma, su tsiro, su girma har su zama itatuwa masu rassa da ganyaye da dama."

1  2  3  4  5  6  7  8  9  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China