Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labaru guda 9 dangane da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kananan yara
2020-06-01 16:02:24        cri

Labari na bakwai: "babban aboki" shi ne "mai sha'awar wasan kwallon kafa"

"Babban aboki" Xi Jinping shi ne wani "mai sha'awar wasan kwallon kafa",

Yana kulawa da ci gaban kwallon kafan matasa sosai.

Ya taba cewa, ya kamata a horar da 'yan wasan kwallon kafa tun daga yarantaka.

A shekarar 2014, a yayin da Xi Jinping ke ziyara a Jamus,

ya tafi filin wasannin motsa jiki na Olimpia na Berlin,

don nuna gaisuwa ga 'yan wasan kwallon kafa matasan Sin dake samun horo a can.

A lokacin, an shirya wata gasa ce a tsakanin 'yan wasan matasa da suka fito daga gundumar Zhidan na lardin Shaanxi

da na kulob din na wasan kwallon kafa na Wolfsburg na Jamus.

"Babban aboki" ya kalli gasar, kuma ya nuna yi tafi da nuna yabo

ga 'yan wasa matasa na Sin da Jamus.

A lokacin hutawa a tsakiyar gasa, Xi Jinping ya shiga tsakanin 'yan wasan,

don fahimtar yadda suke samun horo da zaman rayuwarsu.

'Yan wasan matasa sun yi farin ciki da bayyanawa "mai sha'awar kwallon kafa"

kan kaunar da suke nunawa kwallon kafa, da sakamakon da suka samu wajen horo.

Xi Jinping ya yi farin ciki sosai da cewa,

"ina zura ido kan ku, ina zura ido kan zuriyarku.

Ina fatan za ku kasance taurarin wasan kwallon kafa na duniya."

1  2  3  4  5  6  7  8  9  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China