Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labaru guda 9 dangane da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kananan yara
2020-06-01 16:02:24        cri

 

Ranar 1 ga watan Yuni, wato ranar kananan yara ta duniya

Ranar bikin kananan yara tana tafe-----

A nan kasar Sin, akwai wani babban yaro,

Wanda yake kula da kananan yara.

Ya sha murnar ranar kananan yara ta duniya

A matsayinsa na babban abokin yara.

Yana kuma son zama tare da yara,

Ko da yake yana fama da ayyuka da dama.

Wannan babban abokin yara yana fitowa

A filin wasa, da dakin karatu, wasanni, a ciki da wajen kasar Sin,

Tare da kanana yara.

Wannan babban abokin yara shi ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Labari na farko: Mahaifin dake matukar son diyarsa

Xi Jinping shi ne shugaban kasar Sin, kuma ya kasance wani uba mai nagarta, wanda yake son zama tare da diyarsa.

A kan kantar ajiye littattafai dake cikin ofishinsa, ya ajiye wani hotonsa wanda ya dauka tare da diyarsa, a lokacin da diyar tasa tana karama.

Hoton ya nuna yadda shi da diyarsa suka hau keke, suna wasa tare.

Uwargidan Xi Jinping, Madam Peng Liyuan ta taba waiwaitar kaunar dake tsakanin Xi da diyarsa, inda ta ce, "diyata ta yi kama da shi, kuma tana kaunarsa sosai. Lokacin da take tare da ni, ba ta jin magana. Amma yayin da take zama tare da babanta, to, tana da biyaya da da'a sosai."

1  2  3  4  5  6  7  8  9  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China