Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fannin fasahar ICT a Najeriya ya samar da gudunmawar kashi 14.07 na GDPn kasar a rubu'in farko na bana
2020-06-01 10:22:18        cri
Bangaren fasahar zamani ta ICT a Najeriya ya bada gudunmawar kashi 14.07% na tattalin arzikin GDP a kasar, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya Isa Ali Pantami ya sanar da hakan.

Wannan shi ne karon farko da fannin fasahar ICT na kasar ya samu babban tagomashi, a sanarwar da minista Pantami ya bayar da kwafenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ya ce fannin fasahar ICT ya bayar da gudunmawar kaso mai yawa na GDPn Najeriya a rubu'in farko na wannan shekara, kamar yadda alkaluman hukumar kididdiga ta kasar NBS na baya bayan nan ya bayyana.

Ministan ya danganta nasarorin da fannin fasahar zamani na kasar ya samu da kuma gudunmawar da fannin ya bayar bisa irin jajurcewar gwamnatin tarayyar kasar.

Pantami ya ce, annobar COVID-19 ta kara nuna muhimmancin da fannin fasahar ICT ke da shi ga bunkasuwar tattalin arzikin zamani na Najeriya har ma ga bunkasar tattalin arzikin kasar baki daya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China