2020-06-01 09:59:36 cri |
Alkaluma na nuna cewa, a wannan shekara, baki daya kasar ta ba da takardun lamuni 19,286, matakin da ya taimakawa kamfanoni da gwamnatocin kananan hukumomi tara kudaden da yawansu ya kai Yuan Triliyan 20.1 kwatankwacin dala triliyan 2.82. Kamar yadda kamfanin Wind mai samar da bayanai kan harkokin kudi ya bayyana.
Kamfanin ya ce, a watan Mayun wannan shekara, yawan kudaden da aka tara ta hanyar takardun lamuni, sun kai Yuan Triliyan 3.25.
A wannan shekara, kasar Sin ta hanzarta yadda kananan hukumokin kasar ke raba takardun lamuni, a wani mataki na aiwatar da ayyuka a kan lokaci, don rage tasirin annobar COVID-19.
Bugu da kari, an karfafawa kamfanonin gwiwar amfani da takardun lamuni, a matsayin wata muhimmiyar hanyar tara kudade. Tun da farko alkaluman da babban bankin kasar ya fitar, sun nuna cewa, yawan kudaden da kamfanonin suka tara ta hanyar sayar da takardun lamuni a watan Afrilu, sun tasamma Yuan biliyan 901.5. Karuwar Yuan biliyan 506.6 kan na shekarar da ta gabata. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China