2019-07-16 19:15:55 cri |
Sashen jarin waje na kamfanonin dake hada hadar da ba ta kudade ba, masu jarin waje na kasar Sin ko ODI a takaice, ya samu ci gaba mai armashi cikin watanni 6 na farkon shekarar bana.
Wata sanarwa da ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar a Talatar nan, ta nuna cewa, sashen na ODI na kasashe da yankunan duniya 151, na da darajar da ta kai yuan biliyan 346.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 50.4 a tsakanin wadannan watanni, adadin da ya nuna karuwar da aka samu ta kaso 0.1 bisa dari a shekara guda.
Jami'in hukumar Han Yong, ya ce Sin na ci gaba da gudanar da hadin gwiwa cikin lumana da sauran sassan duniya a fannin bunkasa sashen na ODI cikin watannin 6 na farkon shekarar bana. Ya ce tsakanin wadannan watanni, kamfanonin Sin sun shigar da karin dalar Amurka biliyan 6.8, a fannin zuba jari a kasashe 51 dake kan hanyar ziri daya da hanya daya, adadin da ya kai kaso 12.6 bisa dari na jimillar jarin da aka zuba wa kasashen.(Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China