Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fitch Ratings ya shiga kasuwar hada-hadar takardun lamuni ta kasar Sin
2020-05-15 10:54:04        cri

Sashen gudanarwa na babban bankin kasar Sin ko PBOC, ya yi rajistar kamfanin Fitch Ratings na Amurka, a wani mataki na baiwa kamfanin damar shiga a dama da shi, a hada hadar kasuwannin takardun lamuni na kasar ta Sin.

Hakan dai a cewar PBOC, daya ne daga matakan kara bude kofar kasar ga kamfanoni masu jarin waje, ta yadda za su kara samun zarafin shiga kasuwannin harkokin kudi na kasar.

Wata sanarwar da babban bankin na Sin ya fitar, ta nuna cewa, ita ma kungiyar kamfanonin dake hada hadar zuba jari a kasuwannin hannun jarin kasar, ta karbi takardun kamfanin na Fitch Ratings, na neman wasu harkokin lasafta darajar kasuwar takardun lamuni.

Kamfanin Fitch Ratings, shi ne kamfani na biyu na waje, da ya samu izinin shiga kasuwannin Sin. A shekarar 2019 ne kuma kamfanin S&P Global, ya samu shaidar kasancewa kamfanin waje na farko da Sin ta baiwa izinin shiga kasuwar takardun lamuni na kasar.

Matakin bude sashen kasuwar takardun lamuni ta kasar Sin na cikin muhimman bangarori na fadada kasuwar hada hadar kudade ta kasar. Babban bankin na Sin ya kuma ce zai kara daukar matakan bude kofar sashen, da samar da ci gaba mai armashi a fannin. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China