Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin kudin shigar Sin a farkon watanni shidar bana ya kai triliyan 10
2019-07-16 18:47:47        cri

Yau Talata ma'aikatar kudin kasar Sin, ta fitar da wani rahoto game da kudin shiga, da kudin da aka kashe a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, inda aka bayyana cewa, adadin kudin shigar da aka samu a fadin kasar Sin tsakanin Janairu da Yuni ya kai triliyan 10, adadin da ya karu da kaso 3.4 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Kana an samu karin sakamako a bangaren rage haraji, da kudin da ake biyan hukumomin gwamnatin kasar. Ban da haka kuma, adadin kudin da aka kashe kan rayuwar jama'a wadda ke shafar yaki da talauci, da aikin gona, da raya kauyuka, da manoma, da tsimin makamashi, da kuma kiyaye muhalli ya kai triliyan 12, adadin da ya karu da kaso 10.7 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China