Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin Yada Labaru Na Amurka Da Turai Sun Musunta Labarun Wai Kasar Sin Ta Boye Barkewar Annobar COVID-19
2020-05-27 13:56:46        cri

Kwanan baya, wasu 'yan siyasan kasar Amurka sun yi ta yin shelar cewa, kasar Sin ta boye barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, tilas ne ta dauki alhakin yaduwar annobar a duniya. Dangane da haka, kafofin yada labaru na kasashen Amurka da Turai sun wallafa bayanai da dama don musunta kalaman wadannan 'yan siyasa.

Mujjalar "the National Interest" ta Amurka ta ba da labari a ranar 24 ga wata a shafinta na Internet cewa, matakan da kasar Sin ta dauka sun fi na yawancin kasashe amfani wajen dakile da kandagarkin annobar COVID-19, inda aka dakatar da tafiye-tafiyen mutane tsakanin birane, kowa yana sanya marufin hanci da baki, kana ana aiwatar da kyakkyawan tsarin bincike da bibbiyar mutane masu ruwa da tsaki. Wasu 'yan siyasan kasashen yammacin duniya da wasu kasashen da ke adawa da kasar Sin sun zargi kasar Sin da ta boye barkewar annobar, domin kare kansu kawai a gaban al'umma a gida da kuma matsa wa kasar Sin lamba a ketare.

Haka kuma, wasu kafofin yada labaru na Amurka sun yi nuni da cewa, kasashen Amurka da Turai sun boye yawan wadanda suka harbu da annobar COVID-19. Jaridar New York Times ta labarta cewa, Amurka ba ta tanadi wasu wadanda suka kamu da cutar ba saboda ba a yi musu bincike ba, har ma an mayar da wasu matattun da ake zargin sun mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a matsayin wadanda suka mutu sakamakon cutar mura mai yaduwa.

Har ila yau, jaridar "the Economist" ta ce, sakamakon nazari na kwalejin ilmin kiwon lafiya da cututtukan da aka samu a yankuna masu zafi na London ya nuna cewa, kasashen Birtaniya, Italiya da Spaniya sun gabatar da rahoto kan masu kamuwa da cutar ta COVID-19 da yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 10 ne kawai bisa jimillar wadanda suka kamu da cutar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China