Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karrama wata 'yar Xinjiang wadda ta aikata mummunan laifi da Amurka ta yi ya lalata aikin kare hakkin dan Adam
2020-03-06 20:46:30        cri
Kwanan nan, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta karrama wata 'yar jihar Xinjiang ta kasar Sin, wadda ake zargi da aikata mummunan laifi, mai suna Sayragul Sauytbay da lambar yabo ta "matar dake da jarunta ta duniya" ko kuma International Women of Courage Award a turance, abun da ya ba Amurka damar shafawa kasar Sin kashin kaji kan manufofinta dangane da jihar Xinjiang. A game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Jumma'a cewa, Amurka ta yi biris da gaskiya har tana goyon-bayan wadda ta aikata laifi, abun da ya lalata aikin kare hakkin dan Adam.

Zhao ya ce, wannan 'yar jihar Xinjiang mai suna Sayragul Sauytbay, ta aikata laifuffukan da suka shafi tsallake iyaka ta barauniyar hanya, da yin almundahana ga kudaden bashi, wadda hukumar 'yan sandan Xinjiang ke nema ruwa a jallo. Kana, ba ta taba aiki a cibiyar koyar da sana'o'i a Xinjiang ba, amma ta yi karya da bata sunan jihar Xinjiang domin gudun shari'a da neman mafakar siyasa kawai.

Zhao ya kuma jaddada cewa, a jihar Xinjiang ta kasar Sin, babu wani waje da ake kira "sansanin daurin mutane" kamar yadda ake yada jita-jita. Kuma a cewarsa, mahukuntan Xinjiang na daukar managartan matakai na kawar da ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, ciki har da kafa cibiyar koyon sana'o'in, tare da nufin ganin bayan wadannan matsalolin daga tushe.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China