Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakonnin karfafa gwiwa na Xi yayin tarukan majalisu 2
2020-05-29 13:55:32        cri
Kawar da talauci da daukaka manufar bada muhimmanci ga jama'a, da neman sabbin damarmaki daga kalubale, sun kasance sakonnin karfafa gwiwa da Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gabatar yayin tarukan majalisun kasar 2. .

Kasar Sin ta yanke shawarar kin saita wani buri da take son cimmawa ta fuskar tattatlin arziki a shekarar 2020, maimakon haka, za ta mai da hankali kan kan cimma nasarar yaki da talauci da kammala gina al'umma mai matsakaiciyar ci gaba ta kowacce fuska.

A ranar 24 ga wata, Shugaba Xi ya halarci muhawarar wakilan jama'a daga lardin Hubei na kasar, wanda ya kasance wurin da COVID-19 ta fi kamari.

Ya ce dole ne a tunkari matsalolin dake akwai, da tsara gyare-gyare ba tare da jinkiri ba wajen shawo kan matsaloli, da kalubalen da aka samu daga annobar, yana mai jaddada bukatar inganta tsarin kare lafiyar al'umma.

Da yake halartar zaman wakilan rundunar soji da na 'yan sandan kasar, Shugaba Xi ya yabawa rawar da suka taka wajen yaki da COVID-19, yana mai nanata bukatar cimma muradu da ayyukan karfafa tsaron kasa da rundunonin tsaro a bana.

Ya ba rundunar soji umarnin hasaso yanayi mafi tsanani da inganta horo da shirin yaki da gaggauta tunkarar yanayi masu tsanani da kuma kare 'yanci da iko da tsaro da muradun kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China