Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: Sin za ta yi kokarin samar da isassun guraban ayyukan yi
2020-05-28 21:03:46        cri
A yayin taron manema labarai da aka shirya bayan da aka rufe zama na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, firaministan kasar Li Keqiang ya bayyana cewa, samar da isassun guraban ayyukan yi abu ne mai muhimmanci ga zaman rayuwar al'umma, kana, kasar Sin tana iya bakin kokarinta wajen tabbatar da samar da isassun guraban ayyukan yi, da zuba makudan kudade a wannan fanni.

Firaminista Li ya ce, domin tabbatar da ganin an samar da isassun guraban ayyukan yi, kasarsa ta yarda kananan hukumomi su ragewa kamfanonin kudin haya, da ba su tallafin kudi, da kuma daukar karin wasu matakai don tallafa musu. A bana da kuma shekara mai zuwa, kasar Sin za ta samar da horon sana'o'i ga mutane miliyan 35 ta hanyar amfani da kudaden inshorar aikin da suka rage. Haka kuma kasar za ta kara samar da sabbin guraban ayyukan yi ga jama'a, a bara, an samu karin sabbin kamfanoni dubu 10 a kowace rana a kasar, a bana ma za'a ci gaba da daukar matakai a wannan fanni.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China