Kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana daya daga cikin kasashen duniya da suka samu gagarumin ci gaba cikin kankanin lokaci, lamarin da a kullum ke kara jan hankulan jama'ar duniya. Dangane da haka ne wakiliyarmu Fa'iza Muhammad Mustapha, ta tattauna da Abdullahi Ahmad, wani dalibi dan Nijeriya dake karatu a kasar Sin, don jin ra'ayinsa game da ci gaban kasar. Inda ya fara da bayyana irin abubuwan da suke burge shi game da ci gaban da aka samu a kasar.