Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta fara zamanta na biyu
2020-05-25 20:01:30        cri
A yau ne taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13, ya fara zamansa na biyu.

shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran jagororin kasar sun halarci taron da ya gudana a babban dakin taron jama'a dake Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaban zaunannen kwamitin NPC Li Zhanshu, ya gabatar da rahoton aiki na zaunannen kwamitin NPC na 13.

Bugu da kari, wakilan sun saurari rahoton aikin da shugaban kotun kolin al'umma Zhou Qiang ya gabatar, gami da rahoton da shugaban hukumar koli ta gabatar da kararraki Zhang Jun ya gabatar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China