Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Kwamitin tsakiyar JKS zai kara goyon baya ga lardin Hubei
2020-05-25 08:17:26        cri
A yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shiga tattaunawa da tawagar wakilan lardin Hubei wadda har yanzu ke halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar, inda ya jaddada cewa, ya kamata gwamnatin tsakiya da kamfanoni mallakar gwamnati su kara nuna goyon baya ga lardin Hubei a fannin farfadowa bayan cutar COVID-19, da bada fifiko daga fannin manufofi zuwa ga bada fifiko kan samun ci gaba.

A yayin tattaunawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, muhimmin matsayin da lardin Hubei ke dauka a ci gaban kasa da shiyyar bai canja ba. Ya kamata a taimakawa kamfanoni musamman matsakaita da kananan kamfanoni wajen warware matsalolin da suke fuskanta, da gaggauta fitar da jerin matakan inganta sayayya, da kokarin rage hasarar da aka samu sakamakon yaduwar annobar. Baya ga haka, ya kamata a gudanar da ayyukan samar da aikin yi ga rukunoni ciki har da dalibai masu kammala karatun jami'a, da ayyukan tabbatar da zaman rayuwar al'umma yadda ya kamata, kana da cimma nasarar kammala aikin kawar da talauci ga wadanda har yanzu ke fama da talauci. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China