Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe taro na uku na majalisar NPC karo na 13
2020-05-28 16:14:48        cri

Da misalin karfe 3 da yammacin yau Alhamis, an rufe taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) karo na 13, Xi Jinping da wasu shugabannin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da na gwamnatin kasar sun halarci wannan biki.

Yayin taron, an zartas da kudurin dake shafar rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, da kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2021 mai zuwa, kuma, an zartas da kudurin kafawa da kyautata dokokin kare tsaron kasar dake da nasaba da yankin Hong Kong.

Bugu da kari, an zartas da kudurin aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na shekarar 2019, da shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na shekarar 2020, kuma an amince da shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na shekarar 2020.

Haka zalika kuma, yayin taron, an zartas da wasu daftarin kudurori da daftarin dokoki da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China