Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan NPC sun gabatar da kudirin kafa dokar kare muradun Sinawa da masu zuba jari
2020-05-27 21:52:46        cri
'Yan majalisar NPC sun gabatar da kudirin kafa dokar ba da kariya game da karar da aka shigar kasar kan matakan yaki da COVID-19.

Wakilin NPC Ma Yide, kana mai bincike kan harkokin doka a cibiyar nazarin zaman takewa ta Beijing, ya bayyana cewa, doka za ta taimaka wajen kare 'yanci da muradun Sinawa da masu zuba jari na ketare.

Haka kuma dokar za ta mayar da martani kan yadda ake samun karuwar nuna kiyayya a wasu kasashe kamar Amurka kan kasar Sin game da cutar COVID-19. Ya kuma ba da shawarar cewa, aiwatar da irin wannan doka ta neman kariya, za su hana kai gwamnatoci ketare kara, yayin da aka sha kai gwamnatin kasar Sin kara a kotunan waje, kamar yadda lamarin yake a kasashen Amurka da Canada da Burtaniya da kasashen Turai.

Sama da wakilan majalisar 35 daga Beijing suka nuna amincewa da wannan kudiri, kuma ya samu amincewar zaman da aka yi, har ma an gabatar da shi ga kwamitin majalisar domin ya yi nazari a kai. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China