Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe taron majalissar CPPCC
2020-05-27 16:28:10        cri

An rufe taron majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin ta 13 zama na 3 a yau Laraba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran wasu jagororin kasar sun halarci taron, wanda ya gudana a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.

Shugaban kwamitin kolin majalisar Wang Yang, ya gabatar da jawabi yayin zaman. Kaza lika yayin rufe taron, an amince da kudurin rahoton aikin zaunanne kwamitin koli na majalisar ta CPPCC, da rahoton binciken kudurin kwamitin, da kudurin siyasa game da taron shekara shekara da majalissar ke gudanarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China