2020-05-26 10:56:34 cri |
Sabon ministan kiyaye muhalli na kasar Sin Huang Runqiu, wanda ya kama aiki a karshen watan da ya gabata, ya bayyana a jiya Litinin a nan birnin Beijing cewa, a lokacin aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 don ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, wato daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2025, Sin za ta yi namijin kokarin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da kara kiyaye da farfado da muhalli, ta yadda za a kara zamanintar da tsari da kuma karfin kyautata muhalli.
Yayin da ya zanta da manema labarai a yayin taron shekara shekara na majalisun NPC da CPPCC na bana, Huang Ruiqiu ya ce, kamata ya yi a mai da hankali kan muhimman ayyuka biyu, wato na farko, kara karfin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da kyautata muhalli da kuma takaita wuraren fitar da abubuwa masu gurbata muhalli daga tushe, matakin da ya fi dacewa wajen kiyaye muhalli, na biyu kuma farfado da muhalli da kuma ingiza aikin daidaita ayyukan da suka shafi muhallin tsaunuka, ruwa, gandun daji, gonaki, tabki, da ma filin ciyayi, da kuma kara karfin sa ido kan aikin, ta yadda za a inganta aikin kiyaye muhalli. (Amna Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China