Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta janye daga yarjejeniyar Open Skies
2020-05-22 12:06:53        cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce kasarsa za ta janye daga yarjejeniyar Open Skies, mai ba kasashen da suka amince da ita damar tura jiragen sama domin binciken soji a sararin samaniyar juna. Wannan wani yunkuri ne na Amurka na janyewa daga yarjejeniyar makamai ta kasa da kasa.

Da aka tambaye shi dalili, Donald Trump ya fadawa manema labarai na fadar White House cewa, Rasha ba ta martaba yarjejeniyar, don haka, Amurka za ta fice har zuwa lokacin da za ta fara martabata.

Masana sun bayyana cewa, janyewar Amurka, da aka shafe watanni ana jita-jitarsa, za ta haifar da matsala tsakanin kawayenta na Turai dake cikin yarjejeniyar. Bisa ka'idar yarjejeniyar, janyewar za ta gudana ne cikin watanni 6.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta ce Rasha na jiran tabbacin janyewar Amurka daga yarjejeniyar, kafin mayar da martani.

Yarjejeniyar da ta fara aiki a shekarar 2002, na ba kasashen dake cikinta, damar ba jiragen sama gudanar da bincike a sararin samaniyar juna domin tattaro bayanai game da ayyukan soji.

A yanzu, kasashe 35, ciki har da Rasha da Amurka da wasu na kungiyar tsaro ta NATO ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China