Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai kuskure a cikin wasikar da Trump ya mikawa hukumar WHO
2020-05-20 16:36:21        cri

Mujallar Lancet ta sanar a jiya cewa, akwai kuskure a cikin wasikar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mikawa hukumar lafiya ta duniya wato WHO.

A cikin wasikar, Trump ya bayyana cewa, binciken da gwamnatin kasar Amurka ta gudanar ya gano cewa, hukumar WHO ta yi watsi da bayanan da mujallar Lancet da sauran hukumomin duniya suka bayar a farkon watan Disambar shekarar 2019 ko kafin wannan lokaci, wanda ya bayyana cewa, an samu bullar wata cuta a birnin Wuhan dake kasar Sin.

Babban editan mujallar Lancet Richard Horton ya amsa da cewa, akwai kura-kurai a maganar Trump, mujallarsa ba ta gabatar da rahoto cewar cutar ta fara yaduwa a birnin Wuhan ko sauran wuraren kasar Sin a farkon watan Disambar shekarar 2019 ba, rahoton farko da mujallar ta gabatar game da wannan batu shi ne a ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2020. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China