Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dukkan Muguwar Aniyar Masu Kalubalantar Kwamitin Tsakiyar JKS Game Da Kiyaye Hong Kong Ba Zai Yi Nasara Ba
2020-05-24 16:44:47        cri
Taro na zama 3 na babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 ya duba kudurin gyaran fuska ga dokokin tsaron kasa, masu nasaba da yankin musamman na Hong Kong, lamarin da ya karya lagon makarkashiyar masu neman 'yancin kan Hong Kong da masu adawa da kasar Sin, wadanda suka bata sunan dokoki a cikin 'yan kwanakin nan.

 

 

Wadannan masu tayar da rikici a Hong Kong sun ce, wai dokokin tsaron kasa masu nasaba da Hong Kong za su illata manufar kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu. To, a hakika dai wa ya illata manufar? Dukkan al'ummar yankin Hong Kong da na kasar Sin har ma duniya baki daya sun ga yadda masu nuna karfin tuwo suka sanar da neman 'yancin Hong Kong, da cin mutuncin tutar kasa da kuma kai hari kan 'yan sanda da masu kaunar kasa a Hong Kong. Irin ayyukan na lahanta mulkin kai da tsaro da ci gaban kasa, su ne suka illata manufar kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu.

 

 

Yanzu dai majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta duba dokokin ne da nufin kiyaye manufar, da tabbatar da wadata da zaman karko a Hong Kong da kuma tsaron kasar Sin cikin dogon lokaci, kana da biyan bukatun mazauna Hong Kong na tabbatar da zaman rayuwa cikin lumana.

 

 

A waje guda kuma, kiyaye tsaron kasa da bada tabbaci ga manufar "kasancewar kasa daya da tsarin mulki biyu" nauyi ne dake kan duk al'ummar yankin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China