Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Don me wannan wakiliya daga lardin Hubei ta yi sujada?
2020-05-26 10:47:52        cri

Yayin taron shekara shekara na majalisun NPC da CPPCC na bana, tawagar wakilan lardin Hubei suna tattaunawa kan rahoton gwamnatin kasar Sin. Wata wakiliya cikin wannan tawaga mai suna Yu Cheng ta yi sujada bayan ta ba da jawabi, mene ne ma'anar abin da ta yi?

Yu Cheng wata malama ce daga makaranta ta biyu mai koyar da ilmin masana'antun samar da tufafi na birnin Wuhan, yayin da aka killace birnin sakamakon barkewar cutar COVID-19, ta yi aikin sa kai a cikin unguwa don kulawa da bukatun jama'a a fannin jiyya da zaman rayuwa.

A matsayin wakiliya daga birnin Wuhan, ta gabatar da labarin abokiyarta:

Iyalan abokiyar aikinta mai mutane hudu sun kamu da cutar. Yu Cheng ta ce, da farko, ba su samu gado a asibiti ba, sannan kuma suka tafi asibitin wucin gadi da aka gina cikin gaggawa. Surukin abokiyar aikinta yana cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai a waccan lokaci, inda aka kai shi sashen gobe da nisa na ICU cikin lokaci. A karshe, duk mambobin hudu na iyalan sun warke daga cutar.

A cewar Yu Cheng, Shugaba Xi Jinping ya kai ziyara birnin Wuhan a watan Maris, inda ya nanata cewa, ya kamata a ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'ar Wuhan, ya ce, mazauna birnin na son cin kifi, don haka ya kamata a samar da issasun kifaye bisa halin da ake ciki.

A lokacin killace birnin, an kafa wata hukumar samar da amfanin ruwa, bayan da ma'aikatan unguwannui sun tattara bukatun jama'a na sayayya, hukumar ta samar da kifaye ga gidajensu kai tsaye.

Yu Cheng ta kuma kara da cewa, kafin ta tashi zuwa birnin Beijing, an gaya mata cewa, kamata ya yi ta yi sujada a madadinsu don bayyana godiyarsu ga shugaba Xi Jinping da JKS da kuma kasar, da kuma yin sujada ga wadanda suka baiwa birnin Wuhan taimako. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China