Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guinea-Bissau ta karbi karin gudummowar kayayyakin lafiya daga Jack Ma da gidauniyar Alibaba
2020-05-26 10:42:41        cri
Kasar Guinea Bissau, ta karbi kashi na 3 na gudummowar kayayyakin lafiya daga Jack Ma da gidauniyar Alibaba, wadanda za su taimakawa kasar tunkarar annobar COVID-19

Wata sanarwa da hukumar shirin samar da abinci na duniya (WFP) ta fitar a kasar, ta ce kashin kayayyakin na wannan karo, ya kunshi kayayyakin gwaji 2,496 da abubuwan auna zafin jiki 12 da makarin baki da hanci 28,550 da safar hannu 5,000 da makarin fuska 810 da tabarau 50 da rigunan kariya 1,000 da na'urorin taimakon numfashi 2 da na'urar auna zafin jiki 1.

Kawo yanzu, Guinea-Bissau ta ba da rahoton samun mutane 1,178 da suka kamu da cutar COVID-19, ciki har da mutane 7 da suka mutu da kuma mutane 42 da suka warke. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China