Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko akwai dimokuradiya a kasar Sin?
2020-05-22 15:19:39        cri

Kasashen yammacin duniya su kan bayyana kasar Sin a matsayin wata kasa mai tsarin mulki na kama karya, wai babu dimokuradiya a kasar Sin. Amma shin sun samu wannan ra'ayi ne bisa yin nazari kan tsarin siyasar kasar Sin? Ko kuma kawai suna shafa wa kasar Sin bakin fenti ne saboda kiyayya? Don amsar wadannan tambayoyi, ya kamata mu nazarci wani ginshikin tsarin siyasar kasar Sin, wato tsarin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin.

Tsarin majalisar wakilan jama'a wani babban tsarin siyasa ne na kasar Sin, wanda ya nuna yadda ake ba jama'ar kasar cikakken ikon gudanar da mulki.

Tsarin mulki na kasar Sin ya kayyade cewa, majalisar wakilan jama'ar kasa, ita ce hukumar koli mai kula da harkokin mulkin kasar. Sa'an nan, 'Yan kasa wadanda shekarunsu suka kai 18 da haihuwa, duk suna da damar yin zabe, ko kuma a zabe su don zama wakilan jama'a. Babban iko na majalisar wakilan jama'ar kasar, shi ne ikon kafa dokoki, da na dubawa da tsai da muhimman kudurori, gami da ikon nadawa da tube manyan jami'ai.

A nan kasar Sin, shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman al'umma na wani tsawon lokaci, muhimmiyar manufa ce da ake bukata don neman yalwata zaman rayuwar al'ummar kasar. Sai dai wannan shiri ba zai samu nasara ba, face sai majalisar wakilan jama'ar kasar ta zartas da shi.

Har ila yau, dokokin kasar Sin sun tanadi cewa, wasu manyan shugabannin kasar Sin, irinsu shugaban kasa, da shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasa, dole ne sai majalisar wakilan jama'ar kasar ta zabe su. Haka zalika, majalisar wakilan jama'ar dukkan kasa ce ta ke nada firaministan kasar da kuma ministoci.

Bisa ga wadannan bayanai game da yadda majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ke gudanar da aikinta, za a iya fahimtar cewa, tsarin siyasa na kasar Sin wani salo ne na dimokuradiya, ba tsarin kama karya ba. Saboda jama'ar kasar ne ke zabar wakilansu, sa'an nan wakilan jama'a ne ke da ikon kafa doka da nada manyan jami'ai a kan mukamai, maimakon a mika ikon ga wasu mutane kalilan kawai.

Misali, idan mun dauki taron shekara-shekara karo na 3 na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13 da aka kaddamar a ranar 22 ga wata a nan birnin Beijing, to, za a ga cewa, majalissar tana da iko sosai. A yayin taron nan na kwanaki 7, wanda ake sa ran kawo karshensa a ranar 28 ga watan da muke ciki, wakilan jama'ar kasar Sin 2902 za su tantance rahoton aikin gwamnati, da shirin raya kasa, da tsarin kasafin kudi na bana, da tsarin dokar da ta shafi harkokin jama'a, da rahoton aiki na babban kotun kasar Sin, da dai sauransu. Bayan da wakilan jama'a suka zartas da wadannan daftarori, da manufofi, to, sai kuma su fara yin amfani a matsayin babban kundi da tsare-tsaren da ake bi wajen gudanar da harkokin kasa.

Sa'an nan idan mun kalli rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Li Keqiang ya gabatar, a taron majalissar wakilan jama'ar kasar Sin, to, za mu kara fahimtar wasu manyan fannonin da kasar Sin ta mai da hankali a kai, a kokarinta na raya kasa, a shekarar bara, gami da wannan shekarar da muke ciki.

Ga misali, firaminista Li ya jaddada niyyar gwamnatin kasar ta kafa wata al'umma mai walwala daga dukkan fannoni. Bisa wannan tsari, kasar ta kudiri aniyyar fitar da dukkan mutane masu fama da talauci daga kangin talauci a wannan shekarar da muke ciki.

Sa'an nan yayin da yake tsokaci kan yanayin tattalin arzikin kasar, firaministan kasar Sin ya ce, GDPn kasar Sin, wato yawan kudin kayayyakin da ake samarwa a gida, a shekarar 2019, ya kai Yuan triliyan 99.1, kwatankwacin dalar Amurka kimanin trilian 14, wanda ya karu da kashi 6.1% kan shekarar 2018. Game da shirin raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2020, Mista Li ya ce, ba a tsayar da wani mizani da ake fatan cimmawa a wannan shekarar da muke ciki ba, saboda yanayin bazuwar cutar COVID-19 a duniya ya sa an kasa hasashen ainihin yanayin da tattalin arzikin duniyarmu zai kasance. Amma duk da haka, kasar Sin ta gabatar da wasu matakai don tabbatar da samun zaman karko, da ci gaban tattalin arzikin kasar mai dorewa.

Sauran fannonin da firaministan kasar Sin ya ambata a cikin rahoton da ya gabatar, sun hada da yunkurin tsara wasu dokoki don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankunan musamman na kasar irinsu Hongkong da Macao. Da kyautata tsarin kandagarkin cututtuka, da kara zuba kudi don samar da allurar rigakafin cuta, da magunguna, don tabbatar da lafiyar al'umma. Gami da kokarin rage kudin da gwamnati take kashewa wajen gudanar da harkokinta na yau da kullum, da kara zuba kudi don samar da ayyukan more rayuwar jama'a.

Ta wadannan manufofi ma za mu fahimci cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin kula da jama'a, inda take tallafawa masu karamin karfi, da kula da lafiyarsu, da neman tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, da raya tattalin arziki don amfani dukkan al'ummun kasar. Wannan ya dace da ainihin makasudin tsarin dimokuradiya. Domin tsarin dimokuradiya ba tsari ne na cece-kuce ko kuma cacar baki ba, manufar tsarin ita ce tabbatar da cewa gwamnatin da aka kafa ko aka zabe ta, za ta kula da dukkan muhimman bukatun jama'a. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China