Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin saman Najeriya ta hallaka kusoshin Boko Haram
2020-02-10 21:11:00        cri
Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya Ibikunle Daramola, ya ce rundunar ta yi nasarar hallaka wasu kusoshin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram, wadanda ke taro a wani wuri kusa da dajin Sambisa na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Mr. Daramola ya ce wasu jiragen yakin rundunar sojin kasar ne suka yi barin wuta, kan wata maboyar da aka hakikance jagororin kungiyar na gudanar da taro a ranar Asabar. Ya ce harin ya sabbaba rushewar wasu gine gine, tare da hallaka mayakan kungiyar dake cikin sa, ko da yake dai bai fayyace sunaye, ko yawan mayakan kungiyar, wadanda su rasu ko suka jikkata a yayin harin ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China