|  | 
 | 
| 2020-02-19 10:52:56 cri | 
Ibikunle Daramola, mai magana da yawun rundunar sojojin saman Najeriya ya ce sansanin da aka lalata a yankin Tumbun Zarami, dake daura da kan iyakar tafkin Chadi a jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar, kakakin ya ce sun yi nasarar tarwatsa sansanin ne a ranar Lahadi.
Daramola ya ce, an kaddamar da hare haren ne bayan kammala ayyukan bincike a shiyyar na tsawon kwanaki, inda aka gano hakikanin yankunan, da samun cikakkun bayanan sirri daga majiyoyi masu yawa, ciki har da hedkwatar dakarun rundanar wanzar da tsaron hadin gwiwa.(Ahmad)
| 
 | ||||

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China