Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 8 sun rasu a wani sansanin sojan Nijer sakamakon harin Boko Haram
2020-03-09 10:18:46        cri
Bisa labarin da aka samu daga hukumar tsaron kasar Nijer, a ranar 7 ga wata, kungiyar Boko Haram ta kai hari kan wani sansanin soja dake kudu maso gabashin kasar, harin ya haddasa rasuwar mutane a kalla 8.

Wani jami'in hukumar tsaron kasar Nijer ya bayyana cewa, sansanin da aka kai wa harin, na lardin Diffa dake kudu maso gabashin kasar Nijer. A wannan rana, dakarun kungiyar Boko Haram sun shiga kasar Nijer daga yankin iyakar dake arewa maso gabashin Nijeriya, sa'an nan sun yi musayar wuta da sojojin wannan sansanin na Nijer, lamarin da ya haddasa rasuwar a kalla mutane 8, ciki har da wani kwamandan soja daya da sojoji da dama. Haka kuma, dakarun sun kwashe wasu motoci da makamai daga sansanin.

Yanzu, an riga an kai sojojin da suka ji rauni asibitin dake kusa da sansanin. Kana, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Nijer ba ta fidda sanarwa kan wannan batu ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China