Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu tana shirin dora mutane miliyan 2 kan maganin cutar tarin TB
2019-11-24 15:23:30        cri
Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu David Mabuza ya sanar cewa, kasar tana shirin sanya karin mutane miliyan 2 da suka rage masu dauke da cutar tarin fuka wato TB kan maganin warkar da cutar nan da karshen watan Disambar shekarar 2020.

An bukaci dukkan bangarorin al'ummar kasar da su kara kaimi wajen zakulo mutanen dake dauke da cutar TB wacce ke da alaka da kwayoyin cuta mai karya garkuwar jiki HIV, Mabuza ya bayyana hakan ne a lokacin taron gangamin wuni guda na yaki da cutar Sida na kasar Afrika ta kudun wato (SANAC), wanda aka gudanar a garin Secunda, dake lardin Mpumalanga, domin tunawa da ranar yaki da cutar Sida ta kasa da kasa wacce za'a gudanar a ranar 1 ga watan Disamba.

Yayin da yake jagorantar gangamin na SANAC, Mabuza ya ce, akwai mutanen dake dauke da cutar TB amma ba su taba zuwa an duba lafiyarsu ba.

Mabuza ya ce, an tanadi kayayyakin aikin duba lafiyar mutanen dake dauke da cutar, asibitoci a shirye suke su ba su dukkan kulawar da ta dace a koda yaushe.

Kididdiga ta nuna cewa akwai mutane kusan miliyan 7.4 dake dauke da kwayar cutar HIV a fadin kasar Afrika ta kudu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China