Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan kudi na kasar Sin: Za a kara ware wasu kudade don tallafawa jama'a
2020-05-22 19:50:45        cri
A yau Juma'a ne ministan kudin kasar Sin Liu Kun, ya bayyana cewa kasar za ta aiwatar da muhimman matakai a fannin hada hadar kudi, ciki hadda kara cin bashin gwamnnati da zai haura na bara da kaso 0.8%, da ware wasu kudade daga bangaren kamfanonin mallakar kasa, don shirya tinkarar wasu kalubalolin da za su iya bulla.

Liu ya bayyana hakan ne ga manema labaru, a gefen taron majalissar wakilan jama'ar kasar Sin dake gudana a halin yanzu a nan birnin Beijing. Ya ce za a kuma rage kudin harajin da ake karba, inda wannan ragi zai kai na Yuan triliyan 2.5, don kamfanoni da daidaikun mutane su more wannan sassauci.

Kaza lika gwamnatin tsakiyar kasar, za ta tsuke bakin aljihu, don samar da karin kudi na taimakawa aikin dakile cutar COVID-19, da rage talauci, da aikin ilimi, da kula da tsoffi, da dai makamantansu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China