Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Za a bude taron NPC na shekara shekara a ranar 22 ga watan Mayu
2020-04-29 11:23:20        cri

Zaman zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin da ya gudana tsakanin ranekun 26 zuwa 29 ga watan nan, ya amince da bude taron shekara shekara, na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo 13, tun daga ranar 22 ga watan Mayu dake tafe a nan birnin Beijing.

Sakamakon tabbatar da wannan kuduri a Larabar nan, za kuma a bude taro na 3 na majalissar ba da shawara kan harkokin al'ummar kasar Sin CPPCC karo 13, tun daga ranar 21 ga watan Mayun dake tafe.

Zaman shugabancin kwamitin koli na CPPCC na baya bayan ya tabbatar da goyon baya ga wannan kuduri. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China