Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin tsakiya na kasar Sin sun nazarci sama da kaso 85 na shirye-shirye da shawarwari da 'yan majalisar NPC da ta CPPCC suka gabatar a 2019
2020-05-09 17:35:38        cri
Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta ce ma'aikatu da sassan dake karkashinta, sun kammala nazartar sama da kaso 85 na shirye-shirye da shawarwari da 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da na 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar(CPPCC) suka bayar a 2019.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana yau Asabar, Kakakin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, Xi Yanchun, ta ce hukumomin sun amsa shirye-shirye 7,162 ko kuma kaso 87.8 na jimilar shirye-shiryen da 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar suka bayar da kuma shawarwari 3,281 ko kaso 85 na jimilar shawarwari da 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin sisyasa suka bayar yayin zaman taron shekara shekara na majalisun biyu da ya gudana a watan Maris na 2019.

Sama da shirye-shirye da shawarwari 3,000 sassan majalisar gudanarwar suka amince da su, kana an kaddamar da sama da dabaru da matakai 1,500.

Ta kara da cewa, 'yan majalisar wakilan jama'a da 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa, sun gabatar da sama da shirye-shirye da shawarwari masu amfani 400 yayin da ake fama da cutar COVID-19, da nufin inganta tsarin kiwon lafiyar al'umma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China