Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Rigakafin COVID-19 na Sin zai amfani duniya da zarar ya samu
2020-05-18 20:24:29        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ke kokarin samarwa, zai amfani dukkanin duniya baki daya, da zarar an kammala samar da shi.

Shugaba Xi ya ce, samar da rigakafi, da amfani da shi a cikin gida, tare da gabatar da shi ga sauran sassan duniya, zai zamo gudummawar Sin ga kokarin da ake yi, na samar da isasshen rigakafi, mai sauki ga kasashe masu tasowa.

Xi ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, cikin jawabin da ya gabatar ta kafar yanar gizo, yayin taro na 73, na wakilan dandalin kula da lafiya na daniya karkashin hukumar WHO. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China